Aikin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, wato Chief of Staff?

Sauti 19:49
Ganawar tsohon Shugaban Amurka  Barack Obama da Shugaban Ghana  na wancan lokaci John Evans Atta Mills a fadar shugaban Amurka
Ganawar tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da Shugaban Ghana na wancan lokaci John Evans Atta Mills a fadar shugaban Amurka Reuters/Joshua Roberts

Shirin Tambaya da Amsa na amsa tambayoyi daga masu sauraranmu kan batutuwa da suka shige musu duhu, suke kuma neman karin haske a kai daga nan sashen hausa na Rediyo Faransa Rfi.Za mu soma shirin da wannan tambaya menene ainihin aikin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, wato Chief of Staff? Shin wannan mukamin yana cikin kundin tsarin mulki, wato ko chief of staff a fadar shugaban kasa ko gwamna? Yana da hurumin wakiltar shugaban kasa ko wani minista a wata kasa? Kamar wadanne ma'aikatan ne a karkashinsa?