Afrika

Annobar coronavirus na yiwa 'yan siyasar Afrika dauki dai-dai

Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Najeriya Abba Kyari.
Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Najeriya Abba Kyari. Sahara Reporters

Annobar coronavirus ko kuma COVID-19 dake cigaba da lakume rayuka a duniya ta girgiza Yan siyasar Afirka da kuma jefa su cikin fargaba ganin yadda take musu dauki daidai a kasashe da dama.

Talla

Cikin wadanda cutar ta razana sun hada da shugaban kasar Botswana Mogweetsi Masisi da Firaministan Cote d’Ivoire Amadou Gon Coulibaly da yanzu haka suka killace kan su tare da ministocin da ta harba a kasashen Afirka.

Majiya daga Cote d’Ivoire ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar manyan jami’an gwamnati da dama sun harbu da cutar kuma sun killace kan su.

A Burkina Faso yanzu taron Majalisar ministoci da shugaba Roch Christian Marc Kabore ke jagoranci ana yin sa ne ta bidiyo domin kare kai bayan mutuwar mataimakin shugaban Majalisar Dokoki na biyu Rose-Marie Compaore da kuma samun ministan harkokin waje Alpha Barrry tare da wasu ministoci guda 6 dake dauke da cutar.

A Najeriya an samu rudani a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da aka sanar da cewar Babban Hafsan sa Abba Kyari na dauke da cutar, abinda ya sa aka yiwa shugaban da mataimakin sa Yemi Osinbajo gwaji, wanda ya nuna cewar basa dauke da ita, amma hakan bai hana Osinbajo killace kan sa ba.

Tuni aka tabbatar da Gwamnan Bauchi Bala Muhammed da dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na dauke da cutar.

Shima shugaban kungiyar kasashen Afirka Moussa Faki Mahamat ya killace kan sa bayan gano wani na kusa da shi dake dauke da cutar.

A jamhuriyar dimokiradiyar Congo an ruwaito manyan jami’an gwamnati da daman a dauke da cutar cikin su harda ministan tattalin arziki Acacia Bandubola wanda kanin sa dake rike da mukamin mataimakin Darakta Dedie Bandubola ya mutu sakamakon kamuwa da cutar.

A Kenya gwamnatin Uhuru Kenyatta ta tilasta killace Mataimakin Gwamnan Kilifi Gideon Saburi wanda ya koma gida bayan ya ziyarci Jamus ba tare da killace kan sa ba.

Ga alama wadannan Yan siyasa basa samun goyan baya daga wurin al’ummar kasar su ganin irin sharhin da jama’a keyi dangane da halin da suke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.