Mu Zagaya Duniya

Coronavirus ta lakume rayuka fiye da dubu 20

Wallafawa ranar:

A kasashen Duniya an samu rudani dangane da cutar Coronavirus, wasu kasashe da suka hada da jamhuriyar dimokiradiyar Congo an ruwaito manyan jami’an gwamnati da dama na dauke da cutar cikin su harda ministan tattalin arziki Acacia Bandubola wanda kanin sa dake rike da mukamin mataimakin Darekta Dedie Bandubola ya mutu sakamakon kamuwa da cutar.A Kenya gwamnatin Uhuru Kenyatta ta tilasta killace Mataimakin Gwamnan Kilifi Gideon Saburi wanda ya koma gida bayan ya ziyarci Jamus ba tare da killace kan sa ba.A cikin shirin mu zagaya Duniya Grba Aliyu Zaria ya dubo wasu daga cikin manyan labaren da suka mamaye Duniya kamar dai yadda zaku ji.

Asibitin kula da marasa lafiya a Spain
Asibitin kula da marasa lafiya a Spain Community of Madrid/Handout via REUTERS
Sauran kashi-kashi