Najeriya

An samu karin mutane da suka kamu da Coronavirus a Najeriya

Jami'in likita na gudanar da gwaji dangane da cutar Coronavirus
Jami'in likita na gudanar da gwaji dangane da cutar Coronavirus FRANCK FIFE / AFP

Cibiyar bincike da dakile yaduwar cutuka ta Najeriya, ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar ya kai 81 daga 70, bayan samun karin mutane mutane 11 a jiya Juma’a.

Talla

A karon farko cutar da ta zamewa duniya annoba ta bulla a yankin arewa maso gabashin Najeriya, bayan samun mutane 2 da suka kamu a jihar Enugu.

A Birnin Legas da ya fi ko’ina a Najeriyar adadin wadanda annobar ta shafa, an samu karin mutane 8 da suka kamu, a jimlace kenan adadin a yanzu ya kai 52, yayinda aka gano ragowar mutum guda da ya kamu da cutar a jihar Edo.

Lamarin Coronavirus na shirin durkusar da tattalin arzikin kasashen Afrika,Najeriya sahun gaba domin tilastawa mutane kasancewa a gidajen su ba karamar matsalla ba ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI