najeriya - coronavirus

An samu karin mutane dauke da Coronavirus a Najeriya

Gwajin mutane dake dauke da Coronavirus
Gwajin mutane dake dauke da Coronavirus Simon Wohlfahrt / AFP

Cibiyar bincike da dakile yaduwar cutuka ta Najeriya, ta ce yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar ya karu zuwa 97 daga 81, bayan samun karin mutane da sujka kamu da cutar a jiya asabar.

Talla

An dai gano karin mutanen ne a jihohin Kaduna da Lagas inda mutane 7 suka kamu, yayinda kuma a karon farko aka samu wanda annobar ta shafa a Benue.

A birnin Legas da ya fi ko’ina a Najeriyar adadin wadanda annobar ta shafa a yanzu haka jimillar mutane 59 ne suka kamu da cutar, sai kuma mutane 14 a Abuja.Adadin dake zuwa yan lokuta bayan da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa’I ya bayyana kamuwa da cutar coronavirus da ta zama ruwan dare game duniya bayan kutsawa cikin kasashe 183.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.