Najeriya-Coronavirus

Adadin masu dauke da Covid-19 a Najeriya ya kai 111

Alamar Covid-19,
Alamar Covid-19, (Photo By BSIP/UIG Via Getty Images)

Cibiyar Yaki da Cututtuka a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 ko kuma coronavirus zuwa safiyar yau litinin ya kai 111, sakamakon samun Karin mutane 14 da suka kamu da ita.

Talla

Cibiyar da ke yaki da cututtukan a Najeriya ta ce an samu Karin mutane 9 da ke dauke da cutar a Lagos da kuma wasu guda 5 a Abuja, abin da ya kawo adadin mutanen da suka kamu da ita zuwa 111.

Alkaluman da hukumar ta bayar sun nuna cewar yanzu haka akwai masu dauke da cutar 68 a Lagos, sai 21 a Abuja, yayin da ake da guda 7 a Oyo, guda 3 a Ogun.

Jihohin Edo da Bauchi da Enugu da Osun na da mutane bibbiyu, yayin da ake da mutum guda-guda a Jihohin Ekiti da Kaduna da Rivers da kuma Benue.

Ya zuwa yanzu mutum guda ya rasu, yayin da aka sallami guda 3 da suka warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.