Nijar

Covid-19-Nijar za ta saki fursunoni sama da 1500

Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou ya sanar da sabbin matakai don yaki da cutar Coronavirus a kasar, da suka hada da daukar karin jami’an kiwon lafiya 1,500 a cikin gaggawa, sai kuma sakin fursunoni 1,540 da ke tsare a gidajen yari.

Mahamadou Issoufou, shugaban jamhuriyar Nijar na zantawa da RFI da France 24.
Mahamadou Issoufou, shugaban jamhuriyar Nijar na zantawa da RFI da France 24. ©RFI
Talla

Har ila yau shugaban kasar ya ce gwamnati za ta dauki nauyin biya wa al’ummar kasar wutar lantarki da ruwan sha har tsawon watanni biyu, tare da dakatar da karbar haraji har zuwa watan yuni a duk fadin kasar.

Hakazalika, shugaban kasar ya bayar da umarnin hana fita daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe tsawon makonni biyu cur a birnin Yamai, tare da hana wa mutane fita daga birnin ko bai wa baki damar shiga har tsawon makonni biyu.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da AbdouKarim Ibrahim Shikal ya yi da Alh. Moustapha Kadi na Kungiyar Fararen Hula a Nijar.

Hira ta musamman kan matakin Nijar na sakin fursunoni sama da 1500

Yanzu haka an tabbatar da cewa mutane 22 ne ke dauke da kwayar cutar a kasar da aka samu asarar rayukan mutane 3 yayin da ake sa-ido kan mutane 2,607 saboda yiyuwar yin alaka da wadanda suka harbu da cutar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI