Masu Coronavirus sun tsere a Kamaru
Ministan Kiwon Lafiyar Kasar Kamaru Manaouda Malachie, ya tabbatar da bayanan da ke cewa wasu mutane da dama sun tsere daga wani otal da aka kebe su a birnin Douala bisa zargin cewa suna dauke da cutar Covid-19.
Wallafawa ranar:
Ministan ya ce, mutanen sun shiga kasar Kamaru ne a ranar 17 ga wannan wata na Maris a cikin jirgin saman fasinjan Air France, to sai dai bayan kebe su a wannan otal, mutanen sun yi amfani da matsayinsu na siyasa don ficewa daga wannan otal.
Yanzu haka dai adadin mutanen da ke dauke da cutar ta Covid-19 ya kai 142 a Kamaru, 97 na a birnin Yaoude ne sai kuma 40 a birnin Douala.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu