Adadin wadanda Covid-19 ta kama a Najeriya ya kai 210
Wallafawa ranar:
Cibiyar yaki da cututuka a Najeriya NCDC ta ce adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwar da cutar Covid-19 sun tashi zuwa 4, tare da samun karin mutane 20 da suka kamu da cutar a cikin sa’o’i 24 da baya-bayan nan.
Alkaluma na karshe da hukumar ta wallafa a shafinta cikin daren juma’a, na nuni da cewa a jimilce mutane 210 ne suka kamu da cutar a sassan kasar.
A jihar Lagos ne aka samun wadanda ke dauke da cutar inda adadinsu ya tashi zuwa 109, sai Abuja mai mutane 41, Osun 22, Oyo 8, sai 5 a jihar Akwa Ibom, Ogun na da mutane 4, Edo na da marasa lafiya 7.
Sauran jihohin kuwa su ne Kaduna 4, Bauchi – 3, Enugu – 2, yayin da Ekiti, Ondo, Rivers da kuma Benue kowanne ke da mutum guda-guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu