Covid-19; An samu karin mutane 205 cikin kwana daya a Kamaru
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar lafiya a Kamaru ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar Covid-19 sun kai 509 a halin yanzu, bayan da aka samu sabbin mutane 203 da suka kamu da ita a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Sanarwar da ministan kiwon lafiyar kasar Malachie Manaouda ya fitar a cikin daren jiya juma’a, ta bayyana cewa wannan ne karo na farko da aka taba samun irin wannan adadi a cikin sa’’o’i 24, abin da ke nuni da cewa annobar ta shiga wani mummunan hali a kasar.
Ministan ya ce a halin yanzu dai mutane 8 ne suka rara rayukansu, yayin da wasu 17 suka warke daga cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu