Sojojin Nijar sun kashe 'yan ta'adda 63
Ma’aikatar tsaron jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutuwar sojojin kasar 4 tare da kashe ‘yan ta’adda 63, sakamakon wani gumurzu da aka yi tsakanin bangarorin biyu cikin yankin Tillaberi da ke iyakar kasar da Mali, kamar dai yadda ma’aikatar tsaro ta sanar a daren jiya juma’a.
Wallafawa ranar:
Sanarwar ta ma’aikatar tsaro ta ce an yi arangamar ne da misalin karfe 3 da rabi na rana tsakanin sojojin da kuma ‘yan ta’addar da ke cikin tarin motoci da kuma Babura.
Ma’aikatar tsaron ta ce ko baya ga sojojin kasar 4 da suka rasa rayukansu, akwai wasu 19 da suka samu raunuka.
Wannan dai shi ne gurmuzu na baya-baya da aka yi tsakanin ‘yan ta’addar wadanda ke tsallako iyakar Mali ko Burkina Faso don farmaki a cikin kasar ta Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu