Coronavirus ta kashe tsohon firaministan Libya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Cutar Coronavirus ta kashe tsohon firaministan kasar Libya Mahmud Jibril, wanda ya jagoranci gwamnatin ‘yan tawayen da suka hambarar da Kanar Gadhafi daga karagar mulki a 2011.
Jibril mai shekaru 68 a duniya, ya mutu ne yau ne Lahadi a birnin Alkahira na kasar Masar, kamar dai yadda sakataren jam’iyyarsa Khaled al-Mirimi ya tabbatar.
Marigayin ya shafe tsawon makwanni biyu yana jinya a asibitin birnin Alkahira.
Shi kuwa Sarki Mohammad na 6 na kasar Maroko, a ya bayar da umarnin sakin fursunoni dubu 5 daga gidajen yarin kasar, daya daga cikin matakai don rage cunkoso a wannan lokaci da ake yaki da cutar ta Covid-19.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu