Chadi-Boko Haram

Chadi ta zargi makotanta da nokewa a yaki da Boko Haram

Shugaban Chadi Idriss Deby Itno sanye da kakin soji a fagen-daga da Boko Haram
Shugaban Chadi Idriss Deby Itno sanye da kakin soji a fagen-daga da Boko Haram wotzup.ng

Shugaban Chadi Idris Deby ya ce, daga yanzu dakarunsa ba za su sake shiga wani aikin yaki a wajen iyakar kasar ba, bayan nasarar da suka samu ta murkushe mayakan Boko Haram tare da fatattakar su daga Yankin Tafkin Chadi.

Talla

Deby ya ce, sojojinsa da dama sun mutu a Tafkin Chadi da kuma Yankin Sahel, saboda haka daga yau babu wani sojin Chadi da zai sake zuwa aiki a wata kasa da ke wajen iyakokinsu.

Shugaban ya zargi kasashen da ke fama da matsalar Boko Haram da nade hannayensu, inda suka bar Chadi kadai na yaki da mayakan kungiyar, kuma yanzu haka sun kora wadanda suka rage zuwa cikin Nijar da Najeriya.

Deby ya ce, ya gargadi kasashen da ke makotaka da shi da cewar dakarunsa za su janye daga yankunan da suka kama bayan kakkabe mayakan na  Boko Haram nan da ranar 22 ga watan nan, koda sojojin wadannan kasashe sun shirya karbe iko domin tare yankunan ko kuma a’a.

Kalaman shugaban da aka watsa a tashar talabiji ta kasar na zuwa ne a daidai lokacin da kakakin rundunar sojin Chadi ya sanar da kashe mayakan Boko Haram sama da 1,000 a farmakin da suka kai musu, wanda ya kai ga rasa sojojin Chadi 52.

Dakarun kasar Chadi na cikin kungiyar G5 Sahel da ke yaki da ‘yan ta’adda a Mali wanda ya kunshi dakarun kasashen Burkina Faso da Mali da Mauritania da kuma Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.