Afrika-Coronavirus

'Yan Afrika ta Kudu sun zama salihai saboda coronavirus

Jami'an tsaron Afrika ta Kudu na sintiri kan titi
Jami'an tsaron Afrika ta Kudu na sintiri kan titi Photo: Reuters/Rogan Ward

Ministan ‘Yan sandan Afirka ta Kudu, Bheki Cele, ya ce an samu raguwar aikata miyagun laifuka a cikin manyan biranen kasar sakamakon dokar hana fita da aka kafa don rage yaduwar annobar Coronavirus.

Talla

Ministan ya ce, a cikin kwanaki 9 na farkon fara aiwatar da dokar, an samun raguwar aikatan kisan-kai zuwa 94 sabanin 326 da aka samu a daidai wannan lokaci a bara.

Ministan ya ce, hatta matsalar fyade da ta yi kamari a kasar ta ragu sosai daga 699 da aka samu a irin wannan lokaci a bara zuwa 101 a bana.

A game da sauran laifufuka kuwa da suka hada kwace da hari da makami da dai makamantansu, adadinsu ya ragu zuwa 456 maimakon 2,673 da aka samu cikin kwanaki 9 a bara warhaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI