Magungunan jabu sun cika kasuwannin Afirka-WHO
Wallafawa ranar:
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadi a game da yadda magungunan jabu suka cika kasuwannin kasashen Afirka musamman a daidai wannan lokaci da ake yaki da cutar Covid-19.
Hukumar lafiya ta bayyana cewa wadannan magunguna na jabu an fi samun su ne a kasashen Kamaru, Nijar da kuma Jamhuriyar Dimokuradyyar Congo.
WHO ta bayyana sunayen magungunan har guda 9 wadanda ta ce a cikinsu ne ake samun na jabu da suka hada da Samquine, Niruquine da kuma Chloroquine Phosphate, tana mai cewa ko dai an sarrafa wadannan magunguna a matsayin na jabu ne ko kuma sam ba wani kamfani da aka sani da kwarewa don sarrafa su a hukumance.
Hukumar ta bukaci mahukunta a kasashen na Afirka da su sa ido sosai don hana yaduwar irin wadannan magunguna na jabu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu