Chadi-Boko Haram

'Yan Boko Haram fiye da 40 sun mutu a gidan yarin Chadi

Wasu tsoffin mayakan Boko Haram da sojojin Chadi ta kama
Wasu tsoffin mayakan Boko Haram da sojojin Chadi ta kama REUTERS/Moumine Ngarmbassa

An samu gawarwakin mayakan Boko Haram 43 a cikin gidan yarin Chadi, inda ake tsare da su bayan dakarun kasar sun yi nasarar damke su a wani farmaki da suka kaddamar musu a ‘yan kwanakin nan a zagayen Tafkin Chadi.

Talla

A yayin gabatar da jawabi a gidan talabijin na kasa, mai shigar da kara na gwamnatin kasar, Youssouf Tom ya bayyana cewa, an ga gawarwakin ne kwance a dakin da ake tsare da mayakan.

Rahotanni na cewa, gwajin da aka yi wa hudu daga cikin gawarwakin ya nuna cewa, akwai alamar guba wadda ta haddasa musu bugun zuciya kafin mutuwarsu.

Kodayake har yanzu na ci gaba da gudanar da bincike don gano hakikanin yadda suka mutu a cewar Mr. Tom.

Chadi ta sanar da kashe sama da mayakan Boko Haram dubu 1 a yayin farmakin da ta kai musu a  kwanakin nan karkashin jagorancin shugaban kasar, Idriss Deby wanda aka gan shi sanye da kakin soja a filin-daga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.