Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane 36 a jihar Katsinan Najeriya

Jihar Katsina cikin jan launi a taswirar Najeriya
Jihar Katsina cikin jan launi a taswirar Najeriya Daily Trsut

A Najeriya, ‘yan bindiga sun kai hare-hare a garuruwa da dama da ke yankunan Danmusa, Dutsinma da kuma Safana da ke cikin jihar Katsina inda suka kashe mutane akalla 36 tare da raunata wasu masu tarin yawa.

Talla

‘Yan bindigar sun afka wa kauyuka da dama na wadannan kananan hukumomi a sanyin safiyar jiya asabar, inda suka kashe mutane sannan suka kona gidaje tare da kwashe kadarorin jama’a.

Bayanai sun ce adadin kauyukan da lamarin ya shafa zai kai 10, yayin da shaidu suka ce an kwantar da mutane da dama da suka samu raunuka a babban asibitin garin Dutsinma.

An dai jima ana samun faruwar irin wadannan hare-hare da ake dangantawa da barayin shanu a sassan jihar ta Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI