Coronavirus-Ecowas

Ecowas ta yi nazari kan yadda za ta magance coronavirus

Shugabannin kasashen ECOWAS sun gudanar da taron ne ta kafar bidiyo
Shugabannin kasashen ECOWAS sun gudanar da taron ne ta kafar bidiyo vanguardngr

Shugabannin Kasashen Afrika ta Yamma sun gudanar da taro ta hanyar bidiyo, inda suka yi nazari kan halin da ake ciki dangane da annobar COVID-19 da ke ci gaba da yi wa bil'adama illa a fadin duniya da kuma yadda ta addabi yankin.

Talla

Shugaban kungiyar kuma shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadu Issofou ya janyo hankalin takwarorinsa kan illar cutar ga jama’ar yankin da kuma tattalin arzikinta, inda ya bukaci hadin kai wajen tinkarar matsalar ganin yadda take ci gaba da lakume rayukan jama’a.

Shugaba Issofou ya sake bayyana bukatar yafe wa kasashen Afirka basussukan da ake bin su domin rage radadin wannan bala’i, yayin da ya yaba wa Bankin Raya Kasashen Afirka kan rawar da ya taka wajen yaki da cutar.

Jakadan Majalisar Dinkin Dinkin Duniya na musamman a yankin Mohammed ibn Chambas ya sake jaddada matsayin Majalisar na aiki tare da Kungiyar Kasashen Afirka da kuma ECOWAS wajen tinkarar annobar coronavirus.

Chambas ya bi sahun shugabannin ECOWAS wajen kira a yafe wa kasashen Afirka basussukan da ake bin su.

Shugabannin kasashe 13 suka shiga taron, cikin su har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da sabon shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Embalo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI