Benin

Jamhuriyar Benin ta janye daga kotun Afirka

Shugaban Jamhuriyar Bénin Patrice Talon 10 ga watan afrilun 2017 a birnin Abidjan na (Côte d'Ivoire).
Shugaban Jamhuriyar Bénin Patrice Talon 10 ga watan afrilun 2017 a birnin Abidjan na (Côte d'Ivoire). Sia KAMBOU / AFP

Jamhuriyar Benin ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar amincewa da kotun kare hakkin dan adam ta Afirka, kwana daya bayan da kotun ta bukaci gwamnatin kasar ta jinkirta shirya zaben kananan hukumomi da aka tsara yi ranar 17 ga watan gobe.

Talla

Jagoran ‘yan adawa Sebastien Adjavon ne ya shigar da wannan kasar a gaban kotun da ke birnin Arusha a Tanzania, to sai dai kakakin gwamnatin kasar ta Benin Alian Orounla ya ce sun yanke shawarar janye kasar daga wannan kotu.

To sai dai Marc Bensimhon, lauyan da ke kare Sebastien Adjavon ya ce matakin, wata alama ce da ke tabbatar da cewa gwamnatin kasar ta fara rikidewa zuwa ta ‘yan kama karya.

Karkashin yarjejeniyar da ta kafa wannan kotu, mutum daya, gungun mutane na da damar shigar da kara a gaban wannan kotu domin kalubalantar wani mataki da gwamnatocin kasashensu suka dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI