Najeriya

Jami'an tsaron Najeriya sun kashe 'yan bindiga 89 a Zamfara

Jihar Zamfara a arewacin Najeriya
Jihar Zamfara a arewacin Najeriya Carte/ RFI

Kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa dakarun kasar sun kashe ‘yan bindiga 89 a Gidan Jaja da ke yankin Zurmi a jihar Zamfara, a wani farmakin hadin gwiwa da suka kaddamar kan ‘yan bindigar a jiya asabar.

Talla

Wannan farmaki da aka yi wa take ''Hadarin Daji'', ko baya ga kashe maharan, jami’an tsaron sun ce sun yi nasarar gano babura da makamai masu tarin yawa da maharan ke amfani da su don afka wa jama’a.

Jaridar Daily Trust da ake bugawa a Najeriya, ta ce an kazamfaraddamar da wannan farmaki ne mako daya bayan da ‘yan bindigar suka yi wa jami’an tsaro kwanton bauna inda suka kashe sojoji hudu a wani gandun daji kusa da kauyen Birane da ke yankin na Zurmi.

Wata majiyar ta tabbatar wa jaridar cewa an gano daruruwan shanu da kuma makamai daga hannun ‘yan bindigar lokacin wannan farmaki.

Wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar John Enenche ya sanya wa hannu, ta ce rundunar musamman da ake kira Hadarin Daji tare da taimakon wasu dakarun bataliya ta 35 da kuma wasu dakarun daga runduna ta 17, da jirage masu saukar angulu biyu, sojin sama da kuma ‘yan sanda, sun kai farmaki tare da kashe dimbin ‘yan bindiga a ranar 25 ga watan afrilu a Gidan Jaja.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI