Afrika ta Kudu

Coronavirus: Likitocin Cuba sun isa Afrika ta Kudu don aikin agaji

Tawagar likitoci da jami'an lafiyar kasar Cuba da suka sauka a Afrika ta Kudu.
Tawagar likitoci da jami'an lafiyar kasar Cuba da suka sauka a Afrika ta Kudu. AFP / DIRCO

Fiye da likitocin kasar Cuba hadi da jami'an lafiya 200 sun isa Afrika ta Kudu don tallafawa kasar wajen yakar annobar coronavirus.

Talla

Sanarwar fadar shugaban Afrika ta Kudu ta ce da sanyin safiyar wannan litinin jimillar likitocin tare da jami'an lafiyar na Cuba 217 suka sauka a kasar wadanda suka samu tarba daga manyan jami'an gwamnati.

Shugaban Cyril Ramaphosa yace likitocin na Cuba da suka shahara wajen kai daukin lafiya ga kasashe, za su taimaka matuka wajen yaki da cutar ta COVID-19 musamman a bangaren gwajin gida-gida da gwamnati ta soma a farkon watan Afrilu.

Kawo yanzu dai Afrika ta Kudu ce kasa mafi yawan masu dauke da cutar ta COVID-19 a nahiyar Afrika da adadin mutane dubu 4 da 546. Jami’an lafiya a kasar kuma sun yi nasarar gwajin cutar kan mutane dubu 168 har gida, cikinsu har da dubu 13 a yankin Gauteng da annobar tafi tsananta.

Afrika ta kudu da yanzu ke da jumullar mutum 87 da coronavirus ta kashe ba ita ce kasa ta farko da ta samu tagomashin tallafin jami'an lafiyar na Cuba ba, don ko a farkon watan nan sai da Angola ta tarbi likitoci 250 daga Cuban don tallafa mata yaki da coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI