Burundi: Yakin neman zabe ya kankama duk da barazanar coronavirus

Wasu 'yan kasar Burundi, yayin gangamin siyasa.
Wasu 'yan kasar Burundi, yayin gangamin siyasa. The Independent Uganda

An kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasar Burundi da zai gudana a watan gobe, duk da yadda annobar COVID-19 ke barazana ga shirin.

Talla

‘Yan takarar shugabancin kasar guda 7 ke shirin fafatawa a zaben da zai gudana ranar 20 ga watan Mayu, wanda ya kunshi zaben ‘yan majalisu da na kanana hukumomi.

Ya zuwa yanzu mutane 15 suka kamu da cutar coronavirus a Burundi, kuma mutum guda ya mutu daga cikinsu, yayinda 4 suka warke.

Yanzu haka dai Janar Evariste Ndeyishimiye jam’iyya mai mulki ta CNDD-FDD ta gabatar a matsayin wanda take fatan yam aye gurbin shugaba mai barin gado Pierre Nkrunziza, bayan shafe shekaru 15 yana mulki.

A shekarar 2015 kasar Burundi ta fada cikin tashin hankali mai nasaba da siyasa, bayanda shugaba Nkrunziza ya zarce karo na 3 kan mulkin kasar, abinda ya janyo mutuwar akalla mutane dubu 1 da 200, wasu kimanin dubu 400 kuma suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.