Isa ga babban shafi
Afrika

Matakan dakile coronavirus zai ninka bala'in yunwa a sassan Afrika - MDD

Wani yaro dake cikin dubban 'yan kasar Sudan ta Kudu da suke fuskantar barazanar fadawa cikin bala'in yunwa.
Wani yaro dake cikin dubban 'yan kasar Sudan ta Kudu da suke fuskantar barazanar fadawa cikin bala'in yunwa. AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 min

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewar annobar COVID-19 na shirin jefa wasu kasashen Afirka guda 9 cikin mummunan yanayi sakamakon bala’in yunwar da zasu fuskanta wanda zai ninka cikin watanni 3 kacal.

Talla

Sanarwar majalisar dinkin duniyar ta alakanta karuwar hadarin fuskantar bala’in yunwar, da irin matakan da gwamnatocin kasashen Afrika ke dauka domin dakile annobar coronavirus, ta hanyar killace jama’a da kuma dakatar da hada-hadar yau da kullum, abinda ke tasiri kan fannonin kasuwanci, noma da kuma masana’antu.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar tace matsalar ta rashin abinci a yanzu haka ta shafi mutane akalla miliyan 20, a kasashen da suka hada da Burundi, Djibouti, Habasha, Eritrea, Kenya, Somalia, Sudan ta Kudu da kuma Uganda.

Rahotan ya kuma ce akwai fargabar adadin wadanda za su fada cikin yunwar a nahiyar ta Afrika ya karu zuwa tsakanin mutane miliyan 34 zuwa 43.

A watannin bayan ne dai kasashen Kenya, Somalia, da kuma Habasha suka yi fama da annobar farin dango sama da biliyan 200 da suka rika afkawa gonaki da rumbunansu na abinci.

A karshen watan Janairun da ya gabata hukumar samar da abinci da bunkasa ayyukan noma ta majalisar dinkin duniya FAO ta bayyana kawararar fadin dangon kan Somalia a matsayin mafi muni cikin shekaru 25.

Hukumar ta FAO ta kuma ce hadarin farin dangon da ya taso daga Habasha da Somalia zuwa Kenya, ya kai girman murabba’in kilomita dubu 2 da 400, kwatankwacin girman birnin Moscow na Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.