Dokar hana fita ta janyo karuwar cin zarafin mata a Afrika ta Kudu
Wallafawa ranar:
Bayan shafe makwanni 5 ana mutunta dokar zaman gida a Afrika ta Kudu saboda dakile yaduwar annobar coronavirus, wata ‘yar kasuwa mai sana'ar gyaran gashi ‘Sandy’, ta ce rayuwarta na fuskantar barazana ganin yadda ta kasance killace da mijinta da ya saba cin zarafinta.
‘Yar kasuwar mai shekaru 42 a duniya wadda taki bayyana sunanta na asali, ta ce tun a farkon ranar da aka saka dokar ta soma ganin azaba daga maigidan nata wanda yayi barazanar kashe ta, da wargaza kuma sana'ar da take yi.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce a makwanni 3 na farko baya soma aikin dokar hana fitar a ranar 27 ga watan Maris da ya gabata, sama da mutane dubu 120 ne suka kira layin neman taimakon gaggawa dan agazawa mata da kananan yara masu fuskantar cin zarafi a Afrika ta Kudu, adadin da ya ninka wanda aka saba gani.
Kididdigar jami'an yan sandan kasar ta nuna cewa cikin kowadanne sa’o’i 3, ana kashe mace 1 a Afrika ta Kudun, wadanda mafi akasari mazajensu ke da alhakin halaka su.
Jaridar Daily Maverick ta Afrika ta Kudu ta gargadi cewa baya ga cutar Covid 19 da ta harbi kasar da karfin gaske, matsalar cin zarafin mata da kananan yara ta samu gindin zama a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu