Coronavirus-Afrika

'Yan Afrika miliyan 43 na fuskantar barazanar yunwa saboda COVID-19

Akalla mutane miliyan 43 ke fuskantar hadarin shiga kangin yunwa saboda cutar coronavirus.
Akalla mutane miliyan 43 ke fuskantar hadarin shiga kangin yunwa saboda cutar coronavirus. STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP, tace akalla mutane sama da miliyan 40 dake zaune a Yammacin Afirka za su fuskanci karancin abinci a watanni masu zuwa, sakamakon illar annobar coronavirus wadda ta tilasata killace mutane a cikin gidajen su.

Talla

Rahoton hukumar yace adadin yara 'yan kasa da shekaru 5 miliyan 12 za su gamu da tamowa tsakanin watan Yuni zuwa Agusta sabanin sama da miliyan 8 da aka gani a irin wannan lokaci a shekarar bara.

Wannan ya biyo bayan matakan da gwamnatoci suka dauka na tilastawa mutane zama a gida domin dakile yaduwar annobar coronavirus wadda ta shafi manoma da masu harkar samar da abinci.

Jami’ar dake Magana da yawun Hukumar Elizabeth Byers tace annobar coronavirus ta kuma dada fito da halin da halin kuncin da mutanen da suka bar matsugunin su sakamakon tashin hankali da kuma wadanda sauyin yanayi ya yiwa illa.

Hukumar tace tsakanin watan Yuni zuwa Agusta sama da mutane miliyan 21 zasu sha wahaala wajen ciyar da kan su a Yankin Afirka ta Yamma, musamman a kasashen Gambia da Jamhuriyar Benin.

Byers tace bayan wancan adadi na miliyan sama da 21, wasu miliyan 20 zasu fuskanci matsaloli wajen ciyar da kan su a cikin watanni 6 masu zuwa a sassan Yankin saboda illar da annobar COVID-19 tayi.

Shima kwamishinan kula da Yan gudun hijira na Majalisar Babar Baloch ya bayyana Yankin Afirka ta Yamma da Afirka ta tsakiya a matsayin inda aka fi samun mutanen da aka raba su da matsugunan su ta hanyar tashin hankali wadanda yawan su ya kai sama da miliyan 5 da rabi, yayin da miliyan guda da dubu 300 suka zama ‘yan gudun hijira, yayin da sama da miliyan guda da rabi suka zama wadanda suka rasa kasar da zasu kira kasar su.

Hukumar ta dade tana kira da a tallafawa tarin mutanen da rikicin Yankin Sahel da na Tafkin Chadi ya raba da matsugunan su, tare da wasu sama da dubu 838 da rikicin Burkina Faso ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI