Kamaru

COVID-19 ta jefa mazauna yankin 'yan awaren Kamaru cikin zulumi

Wani yankin garin Buea babban birnin yankin Kudu maso Yammcin Kamaru, bayan farmakin da mayakan 'yan aware suka kai.
Wani yankin garin Buea babban birnin yankin Kudu maso Yammcin Kamaru, bayan farmakin da mayakan 'yan aware suka kai. AFP/File

Al'ummar yankin 'yan aware na Kasar Kamaru sun shiga zulumi sakamakon bullar cutar coronavirus a yankin, wanda a gefe guda yake fama da matsalar rashin tsaro.

Talla

Wani mutum daga kauyen Ekondo dake yankin Kudu maso Yammacin kasar, ya ce muddin ya kamu da coronavirus, toh dole yayi tattaki na tsawon sa'oi 5, sannan ya hau kwale-kwale kafin ya samu isa ga asibiti dan karbar kulawa.

Kungiyoyin agaji sun ce tun a watan oktoban shekarar 2017, sama da mutane dubu 3 suka rasa rayukansu a yankunan Arewa maso Yammaci, da Kudu maso Yammacin kasar ta Kamaru, sakamakon hare-haren ‘yan aware, bayaga wasu mutane 700 da suka tsere daga gidajensu.

Cibiyoyin kula da lafiya sama da 115 ne mayakan ‘yan awaren Kamaru suka lalata, bayaga hare-haren da suke kaiwa jami'an tsaro babu kakkautawa, lamarin da ya jefa al'ummar yankin a cikin halin ha'ula’i na rashin samun kulawa musamman a irin wannan yanayi da ake fama da bullar annobar coronavirus.

A halin yanzu dai, adadin wadanda suka harbu da coronavirus a Kamaru ya kai dubu 2 da 77, yayin da wasu 67 suka sheka lahira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.