Nijar-Madagascar

Nijar ta karbi maganin cutar coronavirus daga Madagascar

Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina yayin kaddamar da ‘Covid-Organics’, magani kuma rigakafin cutar coronavirus na gargajiya.
Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina yayin kaddamar da ‘Covid-Organics’, magani kuma rigakafin cutar coronavirus na gargajiya. RIJASOLO / AFP

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta karbi maganin rigakafin annobar coronavirus daga Madagascar wanda shugaba Andry Rajoelina ya aike mata.

Talla

Babban daraktan ofishin ministan lafiya na Jamhuriyar Nijar Ismaïl Annar ne ya karbi taimakon maganin da Madagascar ta baiwa kasar, wanda ya kasance busashen ganye ne da ake jikawa, domin warkar da mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar da kuma matsayin rigakafin cutar.

Maganin mai suna ‘Covid-Organics’ tsimi ne da aka samar daga 'artemisia’, wani ganye da aka tabbatar da ingancisa a matsayin maganin gargajiya wajen warkar da cutar zazzabin cizon sauro, tare da hadin wasu tsirai na kasar ta Madagascar.

Shugaban kasar Andry Rajoelina ne ya sanar da maganin a matsayin mai warkarwa da kuma rigakafin cutar ta coronavirus.

Saï dai kawo yanzu babu wani binciken kimiya da ya tabbatar da sahihancin maganin na ‘Covid-Organics’ wajen warkar da cutar COVID-19, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.