Coronavirus

Gwamnatin Chadi za ta killace daukacin birnin N’Djamena

Idriss Déby, shugaban kasar Chadi.
Idriss Déby, shugaban kasar Chadi. Ludovic MARIN / AFP

Gwamnatin Chadi tace daga ranar juma’a mai zuwa babu shiga da fita birnin N’Djamena a yunkurin da take dauka domin dakile cutar coronavirus wadda ke cigaba da yaduwa a kasar.

Talla

Sanarwar da gwamnati ta fitar yace ganin mutane 115 da suka kamu da cutar a Chadi sun fito ne daga N’Djamena daga cikin 117 ya zaam dole a dauki matakin kariya, saboda haka motocin daukar abinci kawai da na kayayyaki za’a baiwa izinin shiga da fita birnin.

Ya zuwa yanzu mutane 10 suka mutu sakamakon wannan annoba a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.