'Yan Afrika sama da miliyan 40 na fuskantar hadarin yunwa dalilin COVID-19

Sauti 03:16
Wasu mata manoma a nahiyar Afrika.
Wasu mata manoma a nahiyar Afrika. STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane sama da miliyan 40 dake zaune a Yammacin Afirka zasu fuskanci karancin abinci a watanni masu zuwa sakamakon illar annobar coronavirus wadda ta tilasata killace mutane a cikin gidajen su.Wannan ya biyo bayan matakan da gwamnatoci suka dauka na tilastawa mutane zama a gida domin dakile yaduwar annobar coronavirus wadda ta shafi manoma da masu harkar samar da abinci.Dangane da wannan rahoto Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sakataren yada labaran kungiyar manoman Najeriya kuma kwamishinan Gona a Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Magaji.