Afrika

COVID-19 ka iya kashe 'yan Afrika dubu 190, miliyan 44 kuma su kamu - WHO

Hukumar lafiya ta duniya ta yi hasashen nan da wani lokaci annobar coronavirus za ta iya halaka mutane dubu 190 a Afrika, zalika za ta kama wasu miliyan 29.
Hukumar lafiya ta duniya ta yi hasashen nan da wani lokaci annobar coronavirus za ta iya halaka mutane dubu 190 a Afrika, zalika za ta kama wasu miliyan 29. AFP Photo/Stefanie Glinski

Hukumar Lafiya ta duniya tace rashin daukar matakan da suka dace wajen yaki da annobar COVID-19 ko coronavirus a Afirka, na iya haddasa mutuwar mutanen da adadinsu zai iya kaiwa dubu 83 zuwa dubu 190, yayinda cutar za ta kama mutane tsakanin miliyan 29 zuwa miliyan 44.

Talla

Wannan ya biyo bayan binciken da aka gudanar a kasashe 47 dake Afirka dangane da yadda hukumomi ke tinkarar wannan annoba da kuma yadda cutar ke yaduwa.

Ya zuwa yanzu dai alkaluma sun nuna cewar mutane dubu 2 da 127 suka mutu a Afirka, kuma Masar ke sahun gaba da mutane 495 da suka mutu, sai Algeria mai 490, Moroccota rasa jumillar 183 sannan Najeriya mai 107 ad annobar ta kashe.

Shi dai wannan bincike na hukumar lafiya ya gano yadda cutar ke daukar dogon lokaci kafin ta yadu a Afirka da kuma samun masu karancin shekaru dake kamuwa da ita, sai kuma karancin mutanen dake mutuwa sabanin yadda ake gani a Turai da Amurka.

Binciken ya gano tasirin yanayin kasashen da kuma zamantakewa, a matsayin yadda yake tasiri wajen yada cutar da kuma yawan matasa wadanda suka amfana da rigakafin cututtuka cikin su harda masu yaduwa irin su HIV da tarin fuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.