Tanzania-Coronavirus

Tanzania ta karbi maganin cutar coronavirus daga Madagascar

Wasu dalibai a kasar Madagascar yayin shan tsimin gargajiya na Covid-Organics da shugaban kasar Andry Rajoelina yace magani ne kuma rigakafin cutar coronavirus.
Wasu dalibai a kasar Madagascar yayin shan tsimin gargajiya na Covid-Organics da shugaban kasar Andry Rajoelina yace magani ne kuma rigakafin cutar coronavirus. RIJASOLO / AFP

Tanzania ta karbi kashin farko na maganin gargajiyar da kasar Madagascar ta samar domin magance cutar coronavirus, gami da samun rigakafin kamuwa da ita, wadda kawo yanzu ta addabi duniya.

Talla

Kakakin gwamnatin kasar Tanzania Hassan Abbas ne ya tabbatar karbar maganin a sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter.

Tuni dai Jamhuriyar Nijar ta sanar da karbar nata kason maganin na ‘Covid-Organics’, wanda kasashen Afrika da dama suka bayyana bukatar karbar nasu kason.

Kwararru kan magungunan gargajiya Madagascar sun samar da maganin na Covid-Organics ne daga tsiron shuka na ‘Artemisia’ wanda a baya gwaji ya tabbatar da cewa yana maganin zazzabin malaria.

Sai dai a ranar alhamis da ta gabata hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci gudanar da karin gwaji kan maganin na Madagascar kafin karfafa yin amfani da shi.

A halin da ake ciki mutane 193 suka kamu da cutar coronavirus a Madagascar, 101 kuma sun warke, yayinda har yanzu babu wanda annobar ta kashe a kasar.

Rahotanni daga kasar ta Madagascar sunce sojin kasar sun shiga aikin bi gida-gida suna rabawa jama'a maganin na Covid-Organics, zalika mafi akasarin daliban da suka samu maganin, suna soma sha kafin fara daukar karatu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI