Ghana

Ghana ta zarta kasashen yammacin Afrika wajen yawan masu corona

Wani jami'in tsaro a Ghana, sanye da takunkumin rufe fuska don samun kariya daga cutar coronavirus.
Wani jami'in tsaro a Ghana, sanye da takunkumin rufe fuska don samun kariya daga cutar coronavirus. REUTERS/Francis Kokoroko

Hukumar lafiya ta duniya tace Ghana ta zama kasar dake kan gaba wajen yawan masu cutar coronavirus a yammacin nahiyar Afrika.

Talla

Alklaumman hukumar ta WHO sun nuna cewa yanzu haka jumillar mutane dubu 4 da 263 ne suka kamu da cutar a Ghana, yayinda wasu 2 suka mutu, 378 kuma suka warke.

Hukumar lafiyar tace a rana guda, mutane 921 suka kamu da cutar ta COVID-19 a Ghana, kasa da kwanaki 20 bayan janye dokar hana fita a manyan yankunan kasar na Accra da Kumasi da shugaba Nana Akufo Addo yayi.

A baya Najeriya ke kan gaba wajen yawan masu cutar ta corona a yammacin Nahiyar Afrika, amma hauhawar adadin na Ghana ya maida ta mataki na 2.

Zuwa lokacin wallafa wanna labari Afrika ta Kudu ke kan gaba a nahiyar Afrika baki daya, wajen yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus da adadin dubu 8 da 895, sai Algeria mai mutane dubu 5 da 369, Ghana dubu 4 da 263, Najeriya dubu 4 da 151, yayinda Kamaru ke da jumillar mutane dubu 2 da 274.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI