Bakin Haure

Har yanzu 'yan Afrika na kokarin kwarara zuwa Turai duk da barazanar corona

Wasu 'yan ci rani dake kokarin ratsa Hamada, don isa gabar ruwan Libya, daga nan kuma su ketara tekun Mediterranean don isa Turai.
Wasu 'yan ci rani dake kokarin ratsa Hamada, don isa gabar ruwan Libya, daga nan kuma su ketara tekun Mediterranean don isa Turai. AFP Photo/SOULEMAINE AG ANARA

Bayanai daga hukumomin sa’ido kan iyakokin kasa da kasa da kuma tsaffin masu safarar mutane, sunce har yanzu daruruwan ‘yan Afrika na cigaba da kokarin ketara tekun Mediterranean don isa zuwa nahiyar Turai.

Talla

Rahotanni sunce yawan ‘yan ci ranin da suke kwarara zuwa Turai daga Afrika ya ragu matuka, idan akawa kwatanta da abinda aka gani shekraru 2 zuwa 3 da suka gabata, sai dai har yanzu akwai wadanda basu hakura da aniyar ketara tekun na Mediterranean ba, duk da tsaurara matakan bincike da hukumomin Jamhuriyar Nijar suka yi a yankin Sahara ko Hamadar da ‘yan ci ranin ke bi don isa ga gabar ruwan Libya.

Yanzu haka dai ‘yan ci ranin da suka fi hankoron tserewa matakan tsaron dakile kwararsu zuwa Turai, sun fito ne daga kasashen Gambia, Senegal da kuma Mali, duk da cewa yanzu haka duniya na fuskantar bala’in annobar coronavirus.

Tun a shekarar 2015, hukumomin Turai da na kasashen Afrika da ‘yan ci rani ke ratsawa don isa Turai, suka kafa hadin gwiwa na musamman don dakile kwararar bakin-hauren.

Rahotanni sun ce kimanin makwanni 6 da suka gabata, rundunar sojin Nijar ta kame sama da ‘yan ci rani 300 dake kokarin ketarawa zuwa cikin Libya, yayinda aka sake kame wasu 33 kari a makon jiya.

Sai dai daya daga cikin tsaffin masu safarar ‘yan ci ranin zuwa turai, Salifou Idrissa, yace a baya bayan nan sai da kimanin motoci 60 dauke da ‘yan ci rani suka samu shiga Libya, amma tuni jami’an tsaron kasar suka tsare su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.