Afrika

Bincike ya tabbatar da Akinwumi a matsayin jagora nagari

Akinwumi Adeshina, Shugaban Bankin Raya kasashen Afirka AFDB.
Akinwumi Adeshina, Shugaban Bankin Raya kasashen Afirka AFDB. AFP / Sia Kambou

Wani bincike da aka gudanar kan jagorancin shugaban Bankin Raya kasashen Afirka AFDB Akinwumi Adeshina, dangane da zargin cewa yayi amfani da mukaminsa wajen cika ‘yan Najeriya a Bankin ya wanke shi daga duk wani zargi.

Talla

Wasu ma’aikatan bankin da suka boye sunayen su suka gabatar da takardar korafi mai shafuna 15 ga shugabannin gudanarwar Bankin raya kasashen Afirka inda suke zargin Akinwumi Adeshina da saba ka’idar aiki wajen biyan bukatun kan sa da hana ruwa gudu da nuna san kai wadanda key iwa harkar tafi da bankin illa.

Ma’aikatan sun kuma zargi Adeshina da fifita Yan Najeriya da kuma Najeriyar kan ta wajen tafiyar da bankin inda suke neman ganin an dauki mataki akan sa domin hana shi samun wa’adi na biyu da yake nema, wanda aka shirya zabe a wannan watan, amma saboda annobar COVID-19 aka dage zuwa watan Agusta.

Bayan gudanar da bincike kan lamarin, sakamakon binciken yayi watsi da zarge-zargen wanda ya bayyana a matsayin marasa tushe ballantana makama, wanda hakan ya share masa hanyar samun wa’adi na biyu na karin shekaru 5.

Adeshina na samun goyan bayan kungiyar kasashen Afirka ta Yamma da at Afirka da hukumomin kudade na duniya saboda irin cigaban da ya samarwa Bankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.