Coronavirus-Ghana

Shugaban Ghana ya tsawaita dokar hana tarukan jama’a

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo. REUTERS/Hannah McKay/File Photo

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya tsawaita dokar hana tarukan jama’a da suka hada da na gudanar da ibada da tarukan siyasa, har zuwa ranar 31 ga watan Mayu.

Talla

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar daren jiya Lahadi, shugaba Akufo-Addo yace ya zuwa yanzu an yiwa mutane dubu 160 da 500 gwajin cutar COVID-19, kuma an tabbatar da mutane dubu 4 da 700 suna dauke da ita, yayin da 494 suka warke 22 kuma sun mutu.

Yayain jawabin nasa, shugaban na Ghana yak ara da cewar karin wuraren da dokar hana tarukan ta shafa sun hada da, gidajen rawa, gidajen abinci da shaye-shaye, da kuma bukukuwa.

Zalika haramcin tarukan jana’iza na nan daram sai dai in mutanen da za su halarta basu wuce 25 ba.

Nana Akufo Addo ya kuma jaddada shirin gwamnatinsa na gina manyan asibitoci 88 a fadin kasar cikin shekara 1, kamar yadda ya sha alwashi.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo kan tsawaita dokar hana tarukan jama'a

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.