Kamaru

'Yan awaren Kamaru sun halaka magajin garin Manfe

Marigayi Ashu Prisley Ojong, Magajin Garin Manfe, dake kudu maso yammacin Kamaru masu amfani da turancin Inglishi.
Marigayi Ashu Prisley Ojong, Magajin Garin Manfe, dake kudu maso yammacin Kamaru masu amfani da turancin Inglishi. journalducameroun

Rahotanni daga Kamaru sun ce wasu da ake kyautata zaton ‘yan aware ne a Yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi sun halaka Ashu Prisley Ojong Magajin Garin Manfe, dake kudu maso yammacin kasar, lokacin da suka yiwa tawagar motocinsa kwanton bauna.

Talla

Rahotanni sun ce akwai wasu jami'an soji biyu da suka jikkata sakamakon harin.

Rikici tsakanin dakarun Kamaru da mayakan ‘yan aware ya soma ne tun bayan da gwamnatin kasar tayi amfani da karfin ikonta wajen hana gudanar da zanga-zangar lumana da lauyoyi da kuma malaman makarantu suka yi a shekarar 2016, don nuna fushinsu kan yadda aka mayar dasu saniyar ware.

Tun bayan wannan lokacin akalla mutane dubu 3000 suka gamu da ajalinsu, wasu kusan dubu 750 suka rabu da muhallansu bisa tilas.

Rikicin ‘yan awaren dai ya shafi ma'aikatun lafiya da dama a kasar kafi akasari a yankunan masu amfani da Turancin Ingilishi, inda aka lalata akalla cibiyoyin kula da marasa lafiya 115, bayaga hare-haren da ake kaiwa jami'an kiwon lafiya babu kakkautawa, abinda ke hana mazauna kauyuka samun taimako a lokacin bullar annobar coronavirus.

Kawo yanzu dai Kasar Kamaru na da adadin masu dauke da cutar dubu 2 da 077, bayaga mutane 64 da suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.