Farfesa Balarabe Sani Garko kan shakkun manyan kasashe bisa ingancin maganin corona da Madagascar ta samar

Sauti 03:05
Shugaban Madagascar Andry Rajoelina yayin kaddamar da magani kum rigakafin kamu da cutar coronavirus na Covid-Organics da kwararru a kasarsa suka samar.
Shugaban Madagascar Andry Rajoelina yayin kaddamar da magani kum rigakafin kamu da cutar coronavirus na Covid-Organics da kwararru a kasarsa suka samar. Sarah Tétaud/RFI

Shugaban kasar Madagascar Andyi Rajoelina ya caccaki kasashen duniya kan sukar maganin da kasarsa ta samar na yaki da annobar COVID-19 daga itatuwan gida, inda yake cewa sukar watakila nada nasaba da cewar saboda daga Afirka aka samar da shi.A hira ta musamman da yayi da RFI da kuma Farnce 24, Rajoelina yace ya zuwa yanzu babu koda mutum guda da ya mutu sakamakon COVID-19 a Madagascar, kuma mutane 105 daga cikin 183 da suka kamu da cutar sun warke.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria kuma ga yadda zantawar su ta gudana.