Buhari ya nada Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadarsa
Wallafawa ranar:
Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya nada Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadarsa, don maye gurbin Abba Kyari da ya mutu cikin watan jiya sakamakon fama da coronavirus.
Majiyoyin Labaran Najeriya sun ruwaito sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha na sanar da nadin na Farfesa Gambari yayin taron Majalisar zartaswa da ke gudana yau Laraba.
Farfesa Ibrahim Gambari dan asalin garin Ilirin a jihar Kwara ya rike mukamin ministan harkokin wajen Najeriya a lokacin mulkin Sojan shugaba mai ci Muhammadu Buhari tsakanin shekarar 1984 zuwa 1985.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu