Guinea

Coronavirus: Masu zanga-zanga sun tilasta bude Masallatai a Guinea

Al'ummar Musulmi cikin daya daga cikin Masallatan dake Conakry, babban birnin kasar Guinea.
Al'ummar Musulmi cikin daya daga cikin Masallatan dake Conakry, babban birnin kasar Guinea. Tunisia - Tunisie numerique

Masu zanga-zangar adawa da killace jama’a a gida domin yaki da annobar coronavirus a Guinea, sun yi nasarar tilasta bude Masallatan da aka rufe na makwanni a Conakry, babban birnin kasar.

Talla

Matakin na zuwa ne kwana guda bayan arrangamar da aka yi tsakaninsu da jami’an ‘yan sanda, abinda yayi sanadin kashe mutane 7 dake adawa da shingen hana zirga-zirgar da jami’an tsaron suka kafa a sassa daban daban na birnin Conakry.

Tun daga karshen watan Maris hukumomin Guinea suka sanya rufe Masallatan a matsayin jerin matakan da suka dauka na dakile yaduwar annobar coronavirus a kasar, wadda kashi 80 na jama’arta Musulmai ne.

Shaidun gani da ido sun ce tarin jama’a suka bude Masallacin garin ‘Kamsar’, suka kuma wanke shi kafin gudanar da sallar jam’i, yayinda tarin matasa cikinsu harda mata ke ta yin kabbara a waje.

Daya daga cikin matasan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar tunda gwamnati ta gaza wajen kare lafiyarsu, su sun mayar da hankali wajen Ubangiji wanda shi kadai ke iya kare su.

Wani daga cikin matasan yace abin takaici ne a bude kasuwanni ana hada-hadar saye da sayarwa, yayinda kuma za a rufe Masallatai domin hana ibada, inda yake cewa gara su mutu suna ibada a Masallatai maimakon zama ba tare da sallar ba.

Sakataren kula da harkokin addini a kasar ta Guinea, Jamal Bangoura, ya bukaci yin taka-tsantsan da kuma kwantar da hankali, inda yake cewar an dauki matakin rufe Masallatan ne domin kare lafiyar jama’a.

Rahotanni sun ce akalla mutane dubu 2 da 213 suka harbu da cutar ta COVID-19 a Guinea, yayinda 11 daga cikinsu suka mutu.

Tsakanin shekarar 2013 zuwa 2016 annobar ebola ta kashe mutane dubu 2 da 500 a kasar ta Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.