Lesotho

Lesotho ta zama kasar Afrika ta karshe da annobar COVID-19 ta bulla cikinta

Tutar Lesotho, kasa ta karshe a Afrika da ta sanar da bullar annobar coronavirus a cikinta.
Tutar Lesotho, kasa ta karshe a Afrika da ta sanar da bullar annobar coronavirus a cikinta. AFP

Lesotho ta sanar da bullar cutar coronavirus cikinta, kasar da a baya ta kasance guda daya tilo a nahiyar Afrika da annobar bata shafa ba.

Talla

Ma’aikatar lafiyar kasar tace wanda aka gano yana dauke da cutar na daga cikin ‘yan kasar 81 da suka koma gida daga kasashen Saudiya da kuma Afrika ta Kudu a makon jiya, aka koma yi musu gwajin cutar.

A ranar 29 ga watan Maris da ya gabata Lesotho ta rufe iyakokinta daga shiga ko fita, domin kare kanta daga bullar annobar ta COVID-19, musamman daga makwafciyarta Afrika ta Kudu.

A wani labarin kuma a kasar ta Lesotho, Fira Ministan kasar Thomas Thabane ya bayyana 22 ga watan Mayun da muke ciki, a matsayin ranar da zai yi murabus.

Masu bibiyar lamurran kasar ta Lesotho na ganin matakin Fira Minista Thabane zai kawo karshen matsalolin da kasar ta shafe akalla watanni 6 tana fama dasu, ciki harda rikicin siyasa, da kuma tsamin dangantaka tsakanin bangaren zartaswa da sojojin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI