Coronavirus-WHO

Coronavirus ka iya kashe 'yan Afrika dubu 150 idan ba a tashi tsaye ba - WHO

Wasu 'yan kasar Kenya a birnin Nairobi, yayin jiran yi musu gwajin cutar coronavirus.
Wasu 'yan kasar Kenya a birnin Nairobi, yayin jiran yi musu gwajin cutar coronavirus. AFP / LUIS TATO

Hukumar Lafiya ta Duniya tayi hasashen cewar akalla mutane miliyan 200 annobar coronavirus za ta kama a nahiyar Afirka a cikin shekara guda, yayinda 150,000 za su mutu, muddin hukumomi suka gaza daukar matakan da suka dace wajen dakile annobar.

Talla

Kwararrun da suka gudanar da binciken da aka wallafa a mujallar BMJ Global Health, sun yi hasashen raguwar masu harbuwa da cutar a yankin fiye da sauran sassan duniya kamar Turai da Amurka, da kuma mutane kalilan da ke mutuwa.

Sai dai sun yi gargadin cewa duk da matakan da kasashen Afrika da dama ke dauka wajen kare kawunansu daga annobar cutar, rashin ingantattun ma'aikatun lafiya ka iya haifar da cikas wajen cimma nasara.

Binciken kwararrun na hukumar WHO na zuwa ne a daidai lokacin da ake gargadin annobar COVID-19 ta zama babbar barazana ga bangaren lafiya a kasashe masu tasowa, wadanda kawo yanzu ke fafutuka da sauran manyan cutuka sakamakon tabarbarewar fannin lafiyar kasashen.

Kwararrun sun bayyana kasashen Djibouti, Masar, Morocco, Somalia da Sudan da kuma Tunisia a matsayin wadanda basa fuskantar wata barazana mai girma daga cutar ta coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.