Madagascar

Annobar coronavirus ta kashe mutum na farko a Madagascar

Wata mata dauke kaya a yankin Isotry dake Antananarivo, babban birnin kasar Madagascar. 16/5/2020.
Wata mata dauke kaya a yankin Isotry dake Antananarivo, babban birnin kasar Madagascar. 16/5/2020. © AFP / Rijasolo

Madagascar ta sanar da mutuwar mutum na farko da cutar coronavirus ta kashe a kasar, tun bayan bullar cutar cikinta kusan watanni 2 da suka gabata.

Talla

Ma’aikatar lafiyar kasar tace kafin kamuwa cutar coronavirus ko COVID-19, mutumin mai shekaru 57 na fama da wasu cutukan da suka hada da na sukari, da kuma hawan jini.

Mamacin ma’aikaci ne a wani asibiti dake garin Toamasina dake gabashin kasar ta Madagascar, inda yake lura da filin ajiye motoci.

Kawo yanzu mutane 304 suka kamu da cutar coronavirus a kasar ta Madagascar, 114 sun warke, yayinda mutum guda ya mutu.

Kasashen Afrika da dama ne suka karbi maganin Covid-Organics ta Madagascar ta samar daga saiwar Artemisia, wanda tace gwajin kwararrunta ya nuna, yana warkar da masu coronavirus da kuma bada rigakafin kamuwa da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.