Faransa-Afrika

Faransa ta sanar da kawo karshen amfani da kudin CFA a wasu kasashen Afrika

Wasu mutane yayin hada-hadar cinikayya da takardar kudin CFA a Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast.
Wasu mutane yayin hada-hadar cinikayya da takardar kudin CFA a Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast. REUTERS/Thierry Gouegnon

Gwamnatin Faransa ta amince da kudirin dokar sauya kudin CFA da wasu kasashen yammacin Afrika ke amfani da shi zuwa takardar kudin ECO.

Talla

Majalisar ministocin Faransa ce ta amince da wannan sauyin, amma dole ne a samu amincewar majalisar dokokin kasar.

A karkashin sauyin dai, kudin CFA da kasasashen Afrika fiye da 12 ke amfani da shi, zai ci gaba da rike darajar farashinsa na 655.96 akan takardar kudin Euro.

Kasashen da ke amfani da kudin sun hada da Benin da Burkina Faso da Guinea Bissau da Ivory Coast da Mali da Nijar da Senegal da kuma Togo, dukkaninsu rainon Faransa ne , amma ban da Guinea Bissau.

Sauran kasashe 7 mambobin Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Yammacin Afrika wato ECOWAS, na da nasu takardun kudin daban da suke ci, amma a halin yanzu, ana ci gaba da kokarin ganin duk sun karbi tsarin fara amfani da sabon kudin na ECO.

A cikin watan Disamban da ya gabata, shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara yace, a karkashin yarjejeniyar da suka cimma, Faransa ba za ta yi kane-kane game da lamurran da suka shafi sabuwar takaradar kudin na ECO ba.

Zalika sabon shirin ya bada damar canzar da kudin CFA zuwa Euro ba tare da iyakancewa ba.

Tun a shekarar 1945 aka kirkiri kudin CFA, inda wasu da dama ke ganin cewa, kirkirar kudin wata alama ce dake nuna yadda Faransa ta cigaba da shisshigi cikin lamurran kasashen da ta yiwa mulkin mallaka duk da cewa, sun samu ‘yancinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.