Afrika ta Kudu

Cutar corona ka iya halaka 'yan Afrika ta Kudu dubu 50 a shekarar 2020 - Rahoto

Daya daga cikin likitocin kasar Afrika ta Kudu a harabar cibiyar gwajin cutar coronavirus dake garin Lenasia. 21/4/2020.
Daya daga cikin likitocin kasar Afrika ta Kudu a harabar cibiyar gwajin cutar coronavirus dake garin Lenasia. 21/4/2020. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Wani binciken masana kiwon lafiya a Afrika ta Kudu, ya nuna yiwuwar kasar ka iya fuskantar karuwar yawan mutanen da cutar coronavirus za ta halaka zuwa adadin dubu 50 nan da karshen shekarar 2020 da muke ciki.

Talla

Binciken da masanan suka fitar a jiya Alhamis ya nuna cewa, kasar za ta fuskanci yawan wadanda za su kamu da coronavirus akalla miliyan 3, la’akari da yanayin tsananin sanyin da ke tunkaro kasar bayaga kuskuren jama’a na gaza daukar matakan kariya.

Kawo yanzu dai Afrika ta kudu na da jumillar mutum 339 da coronavirus ta kashe, daga cikin mutune dubu 18 da suka kamu.

Zuwa yanzu dai adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a nahiyar Afrika ya kai dubu 100 da 2, daga cikinsu kuma dubu 3 da 92 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI