Burkina Faso da Ivory Coast sun kaddamar da farmaki kan 'yan ta'adda

Wasu daga cikin dakarun sojin hadin gwiwar Burkina Faso da Ivory Coast
Wasu daga cikin dakarun sojin hadin gwiwar Burkina Faso da Ivory Coast REUTERS/Luc Gnago

Hadin gwiwar rundunonin sojin Burkina Faso da Ivory Coast sun halaka ‘yan ta’adda 8, gami da kame wasu 38, yayin farmakin da suka kaddamar kan sansanonin mayakan masu ikirarin Jihadi akan iyakokin kasashen 2.

Talla

Tun a ranar asabar 23 ga watan Mayu kasashen biyu suka kaddamar da farmakin hadin gwiwar da zummar kawo karshen hare-haren ta'addancin da mayakan ke kaiwa kan yankunan arewacin kasar Burkina Faso da kuma yunkurin afkawa yankunan Ivory Coast.

Kawo yanzu akalla mutane 900 suka rasa rayukansu a Burkina Faso, tun bayan soma fuskantar hare-haren ta’addancin da kasar tayi daga shekarar 2015.

Yayinda ita kuma Ivory Coast mayakan suka soma kai farmaki cikinta a ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2016, inda suka halaka mutane 19, garin Grand-Bissam dake kusa da birnin Abidjan, daga lokacin kuma zuwa yanzu, hukumomin tsaron kasar sun bayyana dakile yukurin kai wasu hare-haren ta’addancin da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.