Afrika

Kungiyar kasashen Afrika ta cika shekaru 57 da kafuwa

Wasu daga cikin shugabannin Afrika da suka kafa kungiyar kasashen nahiyar OAU birnin Addis Ababa na Habasha a shekarar 1963, ciki har da shugaban kasar Ghana Kwame Nkrumah da kuma shugaban Habasha a waccan lokaci, Sarkin Sarakuna Haile Selassie na 1
Wasu daga cikin shugabannin Afrika da suka kafa kungiyar kasashen nahiyar OAU birnin Addis Ababa na Habasha a shekarar 1963, ciki har da shugaban kasar Ghana Kwame Nkrumah da kuma shugaban Habasha a waccan lokaci, Sarkin Sarakuna Haile Selassie na 1 thisisafrica

Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU na bikin zagayowar ranar kafuwarta a ranar 25 ga watan Mayu a shekarar 1963, shekaru 57 da suka gabata.

Talla

A waccan lokacin dai kungiyar kasashen ta nahiyar Afrika na amsa sunan ‘African Unity’ ne a takaice OAU, sunan da aka sauya zuwa ‘African Union' AU a watan Yulin shekarar 2002.

Shugaban kasar Habasha Sarkin Sarakuna Haile Selassie na 1 ne ya soma jagorantar kungiyar ta OAU, bayan kafuwarta a shekarar ta 1963 zuwa 17 ga watan Yuli a 1964, inda Gamal Abdel Nasser shugaban kasar Masar ya karba.

Bikin cika shekaru 57 da kafuwar kungiyar AU na bana da ake yiwa take da ‘Ranar Afrika’ na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke fuskantar annobar coronavirus dake cigaba da halaka dubban rayuka, da kuma tagayyara tattalin arzikin kasashen duniya, ciki harda na nahiyar Afrika, wadanda ke fafutukar neman yafiyar basukan dake kansu, da kuma tallafi daga kasashe masu arziki, domin farfado da tattalin arzikinsu gami da yakar annobar.

A wannan karon bikin kafuwar kungiyar at AU zai gudana ne ta hoton bidiyo ba kamar yadda shugabannin na Afrika suka saba taruwa a wuri guda ba a duk shekara, saboda annobar coronavirus.

Dukkanin shugabannin kasashe da na hukumar gudanarwar kungiyar ta AU, da suka hada da Musa Faki Mahamat, da shugaban kungiyar kuma shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, da sauran masu ruwa da tsaki, za su gabatar da jawabansu ne ta hotunan bidiyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.