Burundi

Ndayishimiye ya lashe zaben shugabancin Burundi

Evariste Ndayishimiye, sabon shugaban kasar Burundi mai jiran gado.
Evariste Ndayishimiye, sabon shugaban kasar Burundi mai jiran gado. AFP

Dan takarar jam’iyyar CNDD-FDD mai mulkin Burundi Evariste Ndayishimiye, ya lashe zaben shugabancin kasar da ya gudana a makon jiya, ranar Laraba 20 ga watan Mayu.

Talla

Yayin bayyana sakamakon zaben a yau Litinin, hukumar zaben kasar ta Burundi, tace Ndayishimiye ya lashe zaben ne da kashi 68.72 na adadin kuri’un da aka kada, yayinda jagoran ‘yan adawa Agathom Rwasa ya samu kashi 24.19 na kuri’un.

Hukumar zabe tace kashi 87.7 cikin 100 na masu katin zabe ne suka kada kuri’unsu yayin zaben shugabancin kasar da jumillar ‘yan takara 7 suka fafata.

Sai dai tuni jagoran ‘yan adawa Agathon Rwasa yayi watsi da sakamakon zaben, inda ya tuhumi gwamnatin shugaba mai barin gado Pierre Nkrunziza da amfani da karfi fiye da kima wajen murkushe ‘yan adawa, bayan da ‘yan sanda suka kame wakilan jami’yyun adawa akalla 200 dake sa idanu kan zaben shugabancin kasar.

A shekarar 2015 rikicin zabe ya barke a Burundi, bayan da Nkrunziza ya lashe zaben shugabancin kasar karo na 3 a jere, abinda ya janyo rasa rayukan akalla mutane dubu 1 da 200, wasu dubu 400 kuma suka rasa rayukansu.

Wannan dai shi ne karo na farko da Burundi za ta samu sauyin shugaban tun bayan darewa bisa mulkin kasar da Pierre Nkrunziza yayi a shekarar 2005.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.