Afrika

Amurka ta bukaci sake bincikar shugaban bankin Afrika

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina.
Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina. PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Kasar Amurka ta bukaci a gudanar da sabon bincike kan zargin aikata ba daidai ba ciki har da fifita wasu tsirarun mutane, da ake yiwa shugaban Bankin raya kasashen Afrika AFDB, dan asalin kasar Nigeria, Akinwumi Adesina.

Talla

A watan jiya ne dai wasu suka rubuta wasikar koke suna zargin Adesina da ayyukan da suka sabawa manufar bankin, tun a lokacin ne hukumar gudanarwar bankin da kuma sauran masu ruwa da tsaki suka kafa kwamitin bincike mai zaman kansa don bin diddigin tuhumar da ake yiwa Adesina.

Bayan gudanar da binciken ne, kwamitin ya wanke Akinwumi Adesina daga zargin dukkanin laifukan da ake masa na karya ka’idoji, da suka hada da baiwa Najeriya fifiko sama da sauran kasashen Afrika, da kuma fifita ‘yan Najeriya wajen basu mukamai a bankin raya kasashen na Afrika AFDB da yake jagoranta. Sai dai tuni masu korafin suka yi watsi da sakamakon binciken.

A baya bayan nan ne kuma, sakataren baitulmalin Amurka Steven Mnuchin ya rubuta takardar neman lallai a gudanar da sabon bincike kan saba dokokin bankin na raya Afrika da ake zargin shugaban bankin yayi.

Wannan dambarwa na zuwa ne a daidai lokacinda Akinwuni Adesina ke neman karin wani wa’adin shugabancin bankin na Afrika na tsawon shekaru 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.