Ibrahim Yakubu, tsohon Ministan harkokin wajen kasar Nijar kan cikar kungiyar AU shekaru 57 da kafuwa

Sauti 03:46
Wasu daga cikin shugabannin Afrika da suka kafa kungiyar kasashen nahiyar OAU birnin Addis Ababa na Habasha a shekarar 1963, ciki har da shugaban kasar Ghana Kwame Nkrumah da kuma shugaban Habasha a waccan lokaci, Sarkin Sarakuna Haile Selassie na 1.
Wasu daga cikin shugabannin Afrika da suka kafa kungiyar kasashen nahiyar OAU birnin Addis Ababa na Habasha a shekarar 1963, ciki har da shugaban kasar Ghana Kwame Nkrumah da kuma shugaban Habasha a waccan lokaci, Sarkin Sarakuna Haile Selassie na 1. thisisafrica

A ranar litinin 25 ga watan Mayu, aka gudanar da bukukuwan zagayowar ranar Tarayyar Afirka, wadda ta yi daidai da cika shekaru 57 da kafa kungiya ta farko don hada kan nahiyar ta Afirka AU.Ibrahim Yakubu, tsohon ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar, ya bayyana muhimmancin ranar Tarayyar ta Afrika, yayin zantawa da AbdoulKarim Ibrahim Shikal.