Burkina Faso

'Yan bindiga sun tilasta rufe makarantu dubu 2,500 a Burkina Faso

Wasu yara mata dalibai kwance a kasa cikin firgici a daya daga cikin dakunan daukar karatunsu dake Dori a Burkina Faso, lokacin da 'yan bindiga suka kawo farmaki. 3/2/2020.
Wasu yara mata dalibai kwance a kasa cikin firgici a daya daga cikin dakunan daukar karatunsu dake Dori a Burkina Faso, lokacin da 'yan bindiga suka kawo farmaki. 3/2/2020. © 2020 Olympia De Maismont/Getty Images

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta ce akalla makarantun boko dubu 2 da 500 aka rufe daga shekarar 2017 zuwa yanzu, sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda a kasar Burkina Faso.

Talla

A rahoton da ta fitar a wannan talata, kungiyar ta ce sama da dalibai dubu 350 ne suka daina daukar darasi sanadiyyar rufe wadannan makarantu lura da yadda ‘yan bindiga ke afka wa jama’a.

Lauren Seibert, daya daga cikin masu bincike a kungiyar ta Human Rights Watch, ta ce ko baya ga malamai da ‘yan bindigar ke afka wa, su ma kansu dalibai da iyayensu na fuskantar irin wannan barazana, lamarin da ya sa mafi yawan mutane suka kaurace wa yankunan da ke fama da rikici, sannan kuma makarantu suka zama kango.

Masu binciken sun gana da jami’an ma’aikatar ilimin kasar ta Burkina Faso, wadanda suka tabbatar da cewa makarantu dubu 2 da 500 ne aka rufe, yayin da ma’aikatar ilimin ta tabbatar da cewa malamai 222 ne suka fuskanci hare-hare ko kuma cin zarafi daga ‘yan bindigar.

A rahoton mai shafuka 114, Human Rights Watch ta ce an kashe malamai akalla 12 a shekarar da ta gabata, sannan kuma wasu da dama aka gallaza masu ta hanyar daure su da mari, aka zane wasu da bulala sannan kuma aka raba wasu da kadarorinsu bayan da suka ki mutunta umarnin ‘yan bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.